Yan Bindiga Sun Aukawa Motocin Malamai a Hanyar Dawowa daga Wa'azi a Nijar

Posted by Martina Birk on Friday, August 23, 2024
  • Shehin malami, Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi bayanin abin da ya faru tsakaninsu da ‘yan bindiga
  • A makon nan wasu miyagun ‘yan bindiga suka tare tawagar malaman a hanyar dawowarsu daga kasar Nijar
  • Malaman sun je Jamhuriyyar Nijar ne domin yin wa’azi, sai ‘yan bindiga suka tare su, amma sun kubuta

Bauchi - Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi wa almajiransa bayani a ranar Laraba, 31 ga watan Agusta 2022 kan harin da aka kai masu a hanyar tafiya.

Shehin malamin addinin ya fahimci akwai bukatar ya yi bayani ne biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa a game da tafiyar da suka yi zuwa kasar ta Nijar.

Jaridar Legit.ng Hausa ta saurari fai-fen jawabin malamin, ya kuma tabbatar da cewa miyagu sun tare tawagarsua hanya, amma babu wani wanda aka rasa.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani kasurgumin dillalin bindiga dauke da makamai zai tafi Zamfara

Kamar yadda Shehin ya fada a jiya, wasu suna ta yada abubuwa masu tada hankali, wanda ba shi ne hakikanin abin da ya faru da su da ‘yan bindiga ba.

Maganar Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

“Kwanaki uku da suka wuce, mun tafi Jamhuriyyar Nijar, mun gabatar da wasu darusa na addini, jiya muka gama darusan da dare. Yau (Laraba) muka fito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gaskiya ne ‘yan bindiga sun tsare mu da safiyar yau. Bayan fitowarmu, muna kan hanya tare da sauran malamai da ‘yanuwa da muka fito gaba daya.Suka zo suka kewaye mu a kan hanya da bindigoginsu, suka tsare. Abin da suka fara yi shi ne kokarin bude motar, amma ba za ta budu ba ta ciki.Da suka ga ba za ta budu ba, sai ku ce za su bude mata (motar) wuta. Ba mu bude mota ba saboda duk mun daidaita a kan ba za a bude mota ba."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun yiwa sojoji kwanton bauna, sun hallaka da yawa a Katsina

- Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

Yadda malamai suka tsira

Ana cikin wannan tirka ne sai shehin yace motar da ke bayansu ta juya da nufin ta kubuta, wannan lamarin sai ya raba hankalin miyagun ‘yan bindigan.

Guruntum yace a nan direbansu ya samu damar tserewa, hakan ya sa miyagun ba su yi nasarar yi wa motocin malaman kofar rago ba, suka yi ta harbe-harbe.

Sheikh Guruntum yace a cikin taimakon Allah babu wanda ya samu rauni ko kwarzane a tawagar malaman, sai dai wasu da abin ya rutsa da su a hanya.

A daina yada labaran karya

Malamin yace jami’an tsaron Nijar sun bada gudumuwar da ta taimaka wajen dakile harin. Shehin ya yi gargadi a game da yada labaran da ba su tabbata ba.

A tawagar malaman akwai shi Sheikh Guruntum da Dr. Mansur Yelwa, da wasu malamai daga jihar Bauchi da Alaranma Abdulraheem Mansur Yelwa.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

Ziyarar Kwankwaso zuwa Kogi

An ji labari ziyarar da Rabiu Musa Kwankwaso ya kai zuwa garuruwan Lokoja da Ogbonicha a Kogi ba suyi armashi ba, domin ya gamu da ‘yan iska.

Wasu sun je har otel, sun rika jifar mutanen ‘dan takaran shugaban kasan NNPP, akasin abin da aka gani a lokacin da ya ziyarci Bauchi da Maiduguri.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC51K2Yp51fZoF5hZRtb2axkZmxonnYmqVmmpmjsaqzwGaqrqORYq62t8CwmGaln6m8pLXNZqSapJGirq95zK6qrqSlo7CqecBmn5qmqZa%2FbrrIo5irZw%3D%3D