- Najeriya ta yi babban rashi yayin da sanata a jamhuriya ta biyu, Sidi Ali, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Alhamis da yamma
- Marigayi, mahaifin muƙaddashiyar kakakin CBN ta ƙasa, Hakama Sidi Ali, ya rasu ne yana da shekaru 96 a duniya
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi ta'aziyyar rasuwar dattijon ƙasar a madadin gwamnati da al'ummar jihar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Tsohon sanata a jamhuriya ta biyu kuma gogaggen dan jarida, Sidi Ali, ya rasu da yammacin ranar Alhamis yana da shekaru 86 a jihar Kano.
Ɗaya daga cikin iyalan tsohon sanatan ne ya tabbatar da haka ga wakilin jaridar Punch ranar Jumu'a, 26 ga watan Afrilu, 2024.
Kwanakin PDP za su zo karshe, tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya sake ficewa
Marigayi Sidi Ali, shi ne mahaifin daraktar sashin sadarwa ta riko a babban bankin Najeriya (CBN), Hakama Sidi Ali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattijon ƙasa marigayi Ali ya yi aiki a cibiyar yan jarida ta Najeriya, ma'aikatar yada labarai da hukumar yada labarai ta ƙasa.
A matsayinsa na dan siyasa mai daraja, ya kasance 'dan jam'iyyar APC kuma ya taka rawar gani a kwamitin dattawan jam'iyyar na jihar Kano.
Gwamnan Kano ya yi ta'aziyya
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi ta'aziyyar wannan rashi ga iyalan marigayin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Jumu'a.
"Na samu labarin rasuwar Alhaji Sidi Ali, a yammacin ranar Alhamis, ya rasu yana da shekaru 86 a duniya."Fitaccen dan siyasar ya kasance amintaccen Jami’in Hulda da Jama’a wanda ya yi aiki tukuru don tabbatar da labaran gaskiya a lokacin yakin basasar Najeriya.APC: Ana tangal tangal da kujerarsa, Ganduje ya fadi wadanda za su iya gyara Najeriya
"Ba za a manta da shi ba bisa gudummuwar da ya bayar a matsayin sanatan jamhuriya ta biyu. A madadin gwamnati da al'umma Kano, ina mika ta'aziyyata ga iyalansa. Allah ya sa Jannatul Firdaus ta zama makwancinsa."- Gwamna Abba Kabir.
Gwamnatin Kano ta fara bincike
A wani rahoton kuma Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta fara binciken dalilan yawaitar mutuwa da ake samu a yan kwanakin nan a kauyuka da biranen jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a Kano, inda ya shawarci al'umma.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbYZ3g49mq6ynmKS7br%2FAp5itmV2otqW1jJqjomWplnqzrdKuZLKZnpZ6pa2MrJ%2Beo5Gnwm6ElWaYZqKZna6zecqapahn