Oluremi Tinubu: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Matar Zababben Shugaban Kasa

Posted by Reinaldo Massengill on Tuesday, August 20, 2024
  • Sanata Oluremi Tinubu, ita ce matar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya a zaɓen 25 ga watan Fabrairu da ya gabata, Bola Ahmed Tinubu
  • Remi Tinubu kuma ita ce sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya a karo na uku
  • Ta yi alƙawarin yin fafutuka don ƙwatowa mata 'yancinsu domin a dama da su a cikin harkokin gwamnati

Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ko kuma Remi Tinubu, uwargidan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Ahmed Bola Tinubu, ita ce sanata mai ci da ke wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dokokin Najeriya.

An haife Remi Tinubu a ranar 21 ga watan Satumba, 1960. 'Yar asalin jihar Ogun ce, kuma ita ce auta a cikin ‘ya’ya 12 a wajen mahaifanta, kamar yadda yake a wani rahoto da Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Canja Fasalin Naira: An Faɗi Matakan da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Gwamnan CBN da Wasu Jiga-Jigai

Ta auri Bola Tinubu a shekarar 1987, inda Allah ya albarkacesu da samun yara 3 a tare. Yaran su ne; Zainab Abisola Tinubu, Habibat Tinubu da kuma Olayinka Tinubu.

Bayanin karatun Oluremi Tinubu

Ta yi karatun sakandire a makarantar 'Our Lady of Apostles' da ke Ijebu-Ode, inda ta rubuta jarrabawar kammala sakandire (WASSCE) a shekarar 1979.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Oluremi ta yi karatun NCE a ɓangaren ilmin tsirrai da dabbobi a kwalejin ilimi ta Adeyemi dake jihar Ondo. Oluremi ta samu digiri a fannin ilimi a jami’ar Ife.

Daga nan ta samu takardar shaidar kammala babbar diploma a kwalejin 'Redeemed Christian Bible' a shekarar 2010.

A shekarar 1999 zuwa 2007, Oluremi ta kasance ita ce uwargidan gwamnan jihar Legas lokacin da mijinta Tinubu, yake gwamna.

Alkawuran da ta yi wa 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Ta Nemi Dakatar da Rantsar da Bola Tinubu

Matar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Oluremi Tinubu a lokacin yaƙin neman zaɓe ta yi alƙawura da dama musamman ma ga matan Najeriya.

Daga ciki akwai fafutukar da ta ce za ta yi na ganin ta ƙwatowa mata 'yanci ta yadda da za a riƙa damawa da su wajen gudanar da ayyuka a ƙasar nan.

Sannan kuma ta bada tabbacin kula da ilimin 'ya'ya mata, wanda ta ce gwamnatin Tinubu za ta ba wa muhimmanci sosai. Sannan akwai bayar da tallafin sana'a ga mata.

Sannan Remi Tinubu ta kuma yi alƙawarin cewa, gwamnatin mijinta za ta yi ƙoƙarin bai wa mata aƙalla kaso 35 cikin 100 a hukumomi da manyan ma'aikatun gwamnati.

Ta ce gwamnatin Tinubu za ta yi adalci sosai ga mata ta hanyar basu damar riƙe manyan muƙamai da kuma tallafa musu da jari don yin sana'o'i.

A wani rahoto da jaridar Leadership ta wallafa, Remi Tinubu ta ce gwamnatin Tinubu/Shettima za ta yi iya bakin kokarinta wajen magance matsalolin mata, da kuma matsalar rashin aikin yi da matasa ke fama da ita.

Kara karanta wannan

Za A Sha Jar Miya: Yan Najeriya Da Kansu Za Su Roƙi Tinubu Ya Yi Tazarce, Betta Edu

Abinda matan Najeriya za su yi tsammani daga gare ta

Da take magana game da abin da matan Najeriya za su yi tsammani daga Oluremi Tinubu, shugabar mata ta jam’iyyar APC ta ƙasa, Dakta Betta Edu, ta ce, ba wannan ba ne karo na farko da ta taɓa riƙe ofishin matar shugaba ba, ta riƙe a Legas.

Haka nan kuma Betta Edu ta ce Oluremi ce mace ɗaya tilo da ta taɓa zuwa majalisar dattawa sau uku a jere, don haka tana da gogewa.

A saboda haka ta ba da tabbacin cewa Oluremi Tinubu za ta yi abinda ya dace a ofishinta na matar shugaban ƙasa.

Kashim Shettima ya bayyana yadda gwamnatin Tinubu za ta kasance

A wani labarin na daban, mataimakin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyanawa 'yan Najeriya irin mulkin da mai gidansa Tinubu zai gudanar.

Ya yi bayanin ne a yayin lakcar shirye-shiryen rantsar da sabuwar gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ0gpRtbGaZkqqvtsPAp2SdmV2urm63wKaYrZldoMJuv8CnoGafkaKybrDAZqSarJGnerutwZqZm52eYsCpwcaamZqmXaCutK2MqKOuqpWitm7AyKesm61f